Jami'in kwastam ya harbi abokin aikinsa da bindiga har lahira bayan ya kuskure mai mota

Wani jami'in hukumar Kwastam ya bindige abokin aikinsa har lahira da safiyar yau a kan tagwayen hanyr Ibadan zuwa Lagos.

Majiyar ISYAKU.COM ta ce lamarin ya faru ne bayan jami'an na Kwastam sun tsayar da wata mota da ke kan hanyarta na zuwa gabacin kasarnan, kuma suka bukaci ya gabatar da takardun mota, amma ya kasa.

Daga bisani sun bukaci mai motar ya biya N300.000 kasancewa kudin harajin motar amma mai motar ya ce kudin sun yi yawa. Daga bisani cacan baki ya kaure tsakanin mai mota da jami'an Kwastam, cikin fushi daya jami'in Kwastam ya dana bindigarsa domi ya harbi mai mota, amma sai ya kuskure shi ya harbi abokin aikinsa wanda ya mutu nan take.

DAGA ISYAKU.COM

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN