Yadda Aisha Buhari ta taka rawa wasu kuma suka mutu domin Buhari ya ci zabe

Allah mai iko, Hausawa sun ce faduwar wani shi ne tashin wani. Yayin da wasu talakawa 'yan Najeriya suka rasa ransu sakamakon murnar shugaba Buhari ya ci zabe kamar wani matashi da ya mutu bayan ya sami hadarin babur yayin da yake murnar cin zabe da Buhari ya yi a garin Jalingo na jihar Taraba.

Shi kuma wani saurayi shiga gwata ne ya yi cikin ruwan kazanta ya yi birgima a ciki kuma ya nuna alamar goyon baya ga shugaba Buhari ta hanyar yin amfani da hannayensa guda biyu wanda ke nuna alamar 4+4.

Ita kuwa uwargidan shugaba Buhari watau Aisha, taka rawa ta yi tare da sauran mata da suka taya ta murnar cin zabe da Buhari ya yi.Fatar mu a nan shi ne, Allah ya sa a wannan zubi na biyu a shugabancin Buhari talakan Najeriya zai more rayuwa kuma kayan masarufi za su yi sauki, tare da samar da ababen more rayuwa ga talaka.


DAGA ISYAKU.COM 

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM 

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN