Yadda Janar Buratai Ya Jagoranci Yaki Da Kansa, Soji Sun Halaka Yan Boko Haram Fiye Da 100

Rahotanni daga rundunar sojin Najeriya sun ce shugaban sojin Najeriya Laftana Janar Tukur Buratai ya jagoranci sojin Najeriya suka kai hari ga 'yan boko haram, kuma suka halaka fiye da mutum 100, yayin da saura suka ranta na kare a jihar Borno.

Janar Buratai ya jagoranci sojin Operation Lafiya Dole da kanshi zuwa fagen daga, tare da taimakon jiragen yakin sojin sama na Najeriya, suka kai hari kan 'yan kungiyar boko haram, lamari da ya haifar da mumunar barna tare da kashe da dama daga cikin 'yan kungiyar.

Babban jami'in hulda da jama'a na rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman, ya shaida haka ranar Litinin, ya kuma kara da cewa sojin sun doshi yankin Tafkin Tchadi , domin sun bi 'yan boko haram da suka tsere suka nufi wannan yanki.

Janar Usman ya ce soji sun kwace makamai masu tarin yawa da yan boko haram suka tsere suka bari a yankunan da soji suka kakkabe 'yan boko haram, da suka hada da Goniri a jihar Yobe, Damasak, Kross Kauwa da Monguno a jihar Borno.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN