Rahotanni daga Abuja sun ce Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya yi ta hawaye da ranar yau, yayin da yake yi wa shugaban kasa Buhari jawabi kan hare haren da 'yan boko haram suke kaiwa a jihar Borno.
Majiyar isyaku.com ta ce, Shettima ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 2:30 kuma ya zarce zuwa wajen taron gaggawa da zai yi tare da shugaba Buhari, wanda ke da nasaba da wni taro na sha'anin tsaro da aka gudanar a jihar Borno ranar Litinin da ta gabata.
Tawagar Gwamnan ta hada da Sanatoci guda uku,'yan Majalisar Wakilai, 'dan takaran kujerar Gwamnan jihar Borno a karkashin jam'iyar APC.
Hakazalika manyan jami'an tsaro na kasa da suka hada da babban Kwamandan askarawan Najeriya, CDS,DSS, NIA, NSA suna cikin taron.
Ana ci gaba da wannan taro kawo yanzu.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi