• Labaran yau


  Rana Ta 6: Muna Nan Daram Har Sai Dino Melaye Ya Mika Kansa Garemu - 'Yansanda

  Yau an shiga rana ta shida kenan jami'an 'yansanda sun ja daga a kofar gidan Sanata Dino Melaye a mashigar titin Sangha da ke unguwar Maitama a Abuja. Yansanda sun ce suna nan daram har sai Sanatan ya fito ya mika kanshi ga 'yansanda.

  Sanata Dino Melaye ya ce baya cikin garin Abuja kuma zai mika kanshi ga 'yansanda idan ya dawo, amma  'yansanda sunn ce sun jiyo muryar Sanatan yana yi ma wani 'dansanda tsawa daga tagar gidansa.

  Tuni jami'an 'yansanda suka kara yawan jami'ai domin ganin Sanatan bai sulale ba. Dino yana 'daya daga cikin Sanatocin da suka dinga yi ma shugaba Buhari ihu a lokacin da yake jawabi a ranar da ya gabatar wa Majalisa kasafi kudi na 2019.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rana Ta 6: Muna Nan Daram Har Sai Dino Melaye Ya Mika Kansa Garemu - 'Yansanda Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama