Gwamnan APC ya ce jam'iyyar ba zata ci zabe a jihar sa ba a zaben 2019


Legit Hausa

Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya bugi kirji ya ce dan takarar gwamna na jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM), Adekunle Akinlade ne zai lashe zabe a jihar. Mr Amosun ya kuma shawarci gwamnatin tarayya kada ta aike da sojoji zuwa jihar domin zabe duk da ya bayar da tabbacin za a gudanar da zaben lami lafiya.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a daren ranar Litinin a taron murnar shiga sabuwar shekara da akayi a Oke-Ilewo a garin Abeokuta. Gwamna Amosun yana takarar kujerar sanata a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress amma yana goyon bayan Mr Akinlade wadda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APM bayan ya sha kaye a hannun Dapo Abiodun.

Mr Amosun ya ce na hannun damarsa, Mr Akinlade zai kayar da Mr Abiodun da sauran 'yan takarar gwamna a zaben da za a gudanar a watan Mayu. Gwamnan mai barin gadon ya yi kira ga al'ummar jihar su rungumi zaman lafiya musamman a wannan lokacin da zabe ke qaratowa.

"Mu hada hannu wuri guda domin nunawa duniya cewa mu mutane ne masu son zaman lafiya kuma jiha ce wadda ta samar da fittatun mutane a Najeriya," a cewar Mr Amosun. "Mu nuna musu cewa bamu bukatar sojoji ko 'yan sanda saboda zabe domin zamu gudanar da zaben mu cikin zaman lafiya da lumana. Sannan ku matasa, duk wanda ya nemi kuyi masa bangar siyasa ke fada masa ya turo yaransu kuyi bangar tare."

A yanzu da ya ke shirin barin mukaminsa na gwamna, Mr Amosun ya mika godiyarsa ga dukkan al'ummar jihar saboda irin gudunmawar da suka bashi har ta kai ga ya samu nasarorin da ya samu a jihar.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN