Legit Hausa
Hukumar sojin sama ta Najeriya mai atisayen Operation LAFIYA
DOLE, ta samu nasarar yiwa wani sansanin 'yan ta'adda na Boko Haram luguden
wuta a garin Baga dake jihar Borno a Arewacin Najeriya kamar yadda jaridar
Premium Times ta ruwaito.
Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar sojin sama
ta Najeriya ta samu nasarar yiwa wani sansani luguden wuta da ya zamto
majalisar kungiyar ta'adda ta Boko Haram a garin Baga da ke jihar Borno. Babban
jami'in hulda da al'umma na hukumar sojin, Ibikunle Daramola, shine ya bayar da
shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a yau Laraba,
inda ya ce hukumar sojin ta aiwatar da wannan bajinta ne a jiya Talata.
Daramola ya yi bayanin cewa, hukumar sojin ta samu nasarar
kai wannan gagarumin farmaki ne a ranar 1 ga watan Janairu na sabuwar shekara,
bayan da jami'an ta na leken asiri suka tabbatar da yadda 'yan ta'adda ke
ribatar wani sansani a garin Baga domin kulla kitimurmurar su.
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar sojin ta yi amfani
da daya daga cikin jiragen ta na yaki mai kirar Alpha Jet wajen yiwa sansanin
'yan ta'addan luguden wuta tare da rugurguza shi. Kakakin hukumar ya kara da
cewa, an samu nasarar yiwa 'yan ta'adda gagarumar barna wajen tarwatsa wannan
sansani tare da dukkanin mazauna cikin sa. A yayin haka jaridar Legit.ng ta
ruwaito cewa, gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi rabon
kudade ga sojoji da ke aikin dawo da zaman lafiya a fadin jihar.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi