Kasa da awa 24 da koransa daga jam'iyar adawa ta PDP, Sanata Babayo Gamawa tsohon shugaban jam'iyar PDP na yankin Arewa, ya bayar da sanarwar canja sheka daga jam'iyar PDP zuwa jam'iyar APC mai mulki. An zargi Babayo ne da yin ayyukan da basu dace da 'dan jam'iya ba.
Bayan koransa daga PDP, Babayo ya je fadar shugaban kasa inda ya sadu da shugaba Buhari, daga bisani kuma ya sanar da canja sheka zuwa APC. A cewarsa, domin ayyukan ci gaba da shuga Buhari ke yi.
Babayo ya ce PDP za ta yi da na sani a kan koran da ta yi masa daga jam'iyar.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi