Kalli Bidiyon Tashin Hankali A Wajen Taron APC A Lagos, Mutum 1 Ya Mutu, Yan Jarida Sun Raunata

Ana fargaban cewa mutum 'daya ya mutu sakamakon tashin hankali da ya barke a wajen kampen na mai neman kujerar Gwamnan jihar Lagos a karkashin jam'iyar APC wanda ake gudanarwa a filin SkyPower ranar Talata, kafin wasu 'yan iska su tayar da hankali da ya sa dole taro ya watse bayan jami'an tsaro sun yi ta harba bindiga a sama.

Wani dan kungiyar NURTW da aka harba a kai mai suna Ismail Hafez ya mutu a Asibitin koyarwa na Jami'an Lagos, bayan an garzaya da shi domin samun kulawan Likitoci bayan harsashi ya same shi a kai.

Hakazalika harsashi ya sami wasu 'yan Jarida guda uku, na The Nation Emmanuel Oladesu, New Telegraph, Temitope Ogunbanke tarae da mai daukar hoton bidiyo na gidan Talabijin na Ibile , Abiodun Yusuf.

Shi ma shugaban kungiyar direbobi na NURTW na Oshodi,  Musiliu Akinsanya a.k.a MC Oluomo, bai tsira ba, domin dai rahotanni sun ce hatta shi ma 'yan iskan sun daba masa wuka a ciki da kuma kansa. Daga bisani 'batagarin sun kwace wa manyan baki da jigajigan jam'iyar APC wayoyinsu na salula da sauran ababe.

KALLI BIDIYO A KASA


DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN