KDF Ta Dira Masarautar Yauri, Don Yekuwa Da Fadakarwa, Karanta Abin Da Ta Ce


Kungiyar ci gaban jihar Kebbi, Kebbi Development Forum ta yi yekuwa tare da wayar da kan jama'a kan muhimmancin karbar katin zabe tare da kada kuri'a lokacin zabe a Masarautar Yauri ranar Alhamis. KDF tare da hadin guiwa da Barewa Youth Initiative, Rural Youth Initiative da kuma kungiyar cigaban Masarautar Yauri YEDA, da kuma wasu kungiyoyi sun sami halartar wannan taron yekuwa.


Shugaban kungiyar cigaban Masarautar Yauri Alhaji Abubakar Umar Warrah, ya albarkaci taron da jawabin fatar alhairi, daga bisani Sakataren kungiyar KDF Alhaji Usman Abubakar Gwandu, ya yi jawabi a madadin shugaban kungiyar KDF Profesa S.D Mahuta, wanda bai sami damar halartar taron ba. Sakataren KDF ya yi jawabi kan manufofin kungiyar da suka shafi wayar da kan jama'ar jihar Kebbi. "KDF wata kungiya ce mai zaman kanta ba ta gwamnati bace, KDF ta kunshi dattiai da kwararru yan asalin wannan jiha masu kishin kai da kuma kishin jihar Kebbi da Najeriya gabadaya".

Sakataren KDF Alh Usman Abubakar ya ce "wadanda basu karbi katin zabe PVC ba su kokarta su je su karba".Ya kuma ce ranar jefa kuri'a fito gabadaya a je a kada kuri'a.Ya kara dacewa "Gwargwadon yawan jama'a gwargwadon muhimmancin da dan suyasa zai ba al'umma. Lokacin kada kuri'a a sa kishin kasa domin kuri'a 'yancinka ce. Mu canza daga kuri'ar meye zan samu daga dan takara.

A nashi jawabin, mukaddashin Kwamishinan zabe na jihar Kebbi wanda Alhaji Usman Adamu ya wakilta, ya yi karin haske kan ababe da suka kamata mai kada kuri'a ya yi a ranar zabe, da kuma ababe da ya kamata a kauracewa aikatawa.

Shi ma a nashi jawabi, babban jami'in 'yansanda mai kula da shiyar Yauri wanda SP Yarima Tanko ya wakilta ya ce " A shirye muke mu tunkari duk wanda ke shirin karya doka a ranar zabe. Yansanda tare da sauran jami'an tsaro a shirye suke tsaf domin ganin sun bayar da cikakken tsaro a ranar zabe".

Wakilin Mai Martaba Sarkin Yauri, wanda Rukuban Yauri Alhaji Usman Hassan ya wakilta, ya yaba wa shugabanni da manbobin KDF bisa wannan namijin aikin wayar da kan jama'a  da suke yi tare da sa albarka cikin lamarin.

Daga cikin wa'danda suka halarci taro, har da wakilin Sarkin Yauri wanda shi ne Rukuban Yauri Alh. Usman Hassan, Sakataren KDF na jihar Kebbi Alh. Usman Abubakar Gwandu, shugaban YEDA Alh. Abubakar Umar Warrah, Wakilin Kwamandan 'yansanda shiyar Yauri SP Yarima Tanko da wakilin D.O na  NSCDC,wakilan NPS, sauran kungiyoyi da kuma kungiyoyin mata tare da dimbin jama'a maza da mata.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN