Gwamnatin jihar Kebbi tace ta kashe Naira biliyan 2 wajen
samar da benci da kujerun zama ga makarantun firamare da sakandare a jihar don
bunkasa ingancin ilimi. Kwamishinan jihar na ilimin farko da sakandare,
Magawata Aliero, ya sanar da manema labarai a Birnin Kebbi a ranar laraba cewa
an kashe kudaden ne tsakanin 2015 zuwa 2018.
"A kokarin gwamnatin don kara inganta ilimi, ta gyara
tare da samar da sababbin azuzuway, bencina da kuma kayan aiki ga malamai da
dalibai don inganci. Tsakanin 2015 zuwa yau, gwamnatin jihar ta kashe sama da
Naira biliyan 2 akan dalibai da malaman firamare da sakandare," inji shi.
Mista Aliero yace litattafan karatu da saurany na koyarwa sun kai na kimanin
Naira miliyan 600 da gwamnatin jihar ta siya a 2018.
" Yace gwamnatin ta gina tsangaya guda 6 ta makarantar
firamare, makarantun hadakar koyar da Qur'ani guda 504 da makarantun fulani
makiyaya 40, wadanda duk an cika su kayayyakin karatu da koyarwa da kuma koyon
sana'a.
"Wadannan
sana'o'in zasu taimaki matasan da suka gama manyan makarantu su zama masu
dogaro da kansu, tare da rage yawan rashin aikin yi a jihar," inji
kwamishinan. Mista Aliero yace gwamnatin jihar ta dau tsatsauran mataki wajen
rage shaye shayen kwayoyi a tsakanin daliban jihar ta hanyar shirya taron wayar
da kai da karawa juna sani.
"Jami'an bada shawara da wasu malamai an horar dasu
karkasy shirin tare da hadin guiwa da ma'aikatar ilimi ta tarayya da majalisar
dinkin duniya," inji shi. Kwamishinan ya hori malamai da su tabbatar da
sun koyar da ingantaccen ilimi a makarantu da kwalejojin jihar.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi