Gwamnonin APC 22 Basu Halarci Taron Majalisar Kaddamar Da Zaben Shugaban Kasa PCC Ba

Gwamnoni guda 22 na jam'iyar APC basu halarci taron kaddamar da majalisar kaddamar da zaben shugaban kasa PCC ba da ake gudanarwa yanzu haka a fadar shugaban kasa.

Daily Trust ta ruwaito cewa sauran manbobin majalisar sun halara saidai Gwamnonin APC ne kadai basu zo ba, a taro da ake gudanarwa yanzu haka a dakin taro na fadar shugaban kasa.

Bayanai sun ce ana sa ran cewa Gwamnoni ne za su zama jagoran shirin a jihohinsu.

Gawamnonin jam'iyar APC a jihohi 22 na tarayyar Naajeriya sun hada da:

Adamawa, Bauchi, Borno, Yobe, Kano, Kaduna, Zamfara, Katsina, Kebbi, Jigawa, Niger, Plateau, Nasarawa, Kogi, Lagos, Ondo, Ekiti, Osun, Ogun, Oyo, Edo; Imo.

Shugaba Buhari ya ce makasudin taro shi ne domin a yi la'akari tare da amincewa da tsare tsare na yadda za a tafiyar da majalisar campen na shugaban kasa.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN