Type Here to Get Search Results !

An Bizine Jigon Kungiyar NURTW Da Aka Kashe A Wajen Taron APC A Jihar Lagos | ISYAKU.COM

An bizine gawar wani jigo a kungiyar matuka motocin haya na NURTW Ismaila Azeez Ibrahim wanda aka kashe a wajen wani taro na kaddamar da 'dan takarar kujerar Gwamna a karkashin jam'iyar APC a jihar Lagos ranar Talata 8 gawatan Janairu 2019.

Mun kawo maku rahotun yadda ake zargin wasu 'yan iska daga kungiyar NURTW wadanda basa jituwa da daya bangare na kungiyar suka shiga filin SkyPower wajen da ake taron na APC dauke da bindigogi, wukake, adduna da sauran muggan makamai, sakamakon haka suka haifar da rudani da ya kai ga tashin hankali da ya sa jami'an tsaro suka yi kokarin shawo kan lamarin, amma sai 'yan iskan suka fara harbe harbe da bindigogi.

Sakamakon haka taro ya watse, da misalin karfe 1:30 domin Gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Lagos yana tsakar jawabi ne 'yan iskan suka shigo filin dauke da wa'dannan muggan makamai, ala tilas Gwamna Ambode ya katse jawabinsa kuma jami'an tsaro suka bashi kariya tare da mataimakiyarsa Mrs Idiat Adebule tare da 'dan takaran kujerar Gwamna a karkashin jam'iyar APC a jihar Lagos Mr Babajide Sanwoolu suka fice daga filin taron.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN