Tsohon Sarkin Gwandu Jokolo,Ya Bayyana Yadda Dasuki Ya Dora Buhari Kan Mulki A 1983

Wannan wani rahoto ne wanda jaridar Dailynigerian ta wallafa, kuma UMAR A. HUNKUYI ya fassaro mana. Rahoton yayi cikakken bayani kan yadda dasuki ya daura buhari a mulki a shekarar 1983. Ga cikakken rahoton: Tsohon dogarin Janar Muhammadu Buhari, lokacin da ya Shugabanci kasarnan a mulkin Soja, Mustapha Jokolo, ya fasa kwai kan irin rawar da wani tsohon mai baiwa Shugaban kasa shawara Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ya taka wajen samun nasarar juyin mulkin da Sojoji suka yi a shekarar 1983, wanda shi ne ya dora Buhari, a matsayin Shugaban kasarnan na mulkin Soja a wancan lokacin. Mustapha Jokolo, wanda tsohon Sarkin Gwandu ne wanda aka tube, ya yi wadannan bayanan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da wata jarida, a martanin da yake mayar wa kan wani littafi da Sarkin da ya gaje shi a Sarautar ta Gwandu, Janar Muhammadu Iliyasu Bashar mai ritaya, ya rubuta. A cewar tsohon Sarkin Jokolo, Dasukin ya taka mahimmiyar rawa ta hanyar daukan nauyin juyin mulkin da kudin sa da kuma kitsa yadda juyin mulkin wanda a cikin sa ne Muhammadu Buhari ya zama Shugaban kasa, zai yi nasara a 1983. Da yake magana kan wasu bayanai da ke cikin littafin na Janar Bashar, Jokolo, ya nanata maganan na shi inda yake cewa, “A bisa zahirin gaskiya, wannan shi ya sanya nakan ji zafi sosai kan halin da Dasukin yake ciki a halin yanzun. Na damu sosai da hakan. “Wannan gaskiyan kenan. Baccin na kawo Dasuki, cikin lamarin juyin mulkin ba, na 1983, da juyin mulkin da Buharin ya zama shugaban kasa a cikin sa bai yi nasara ba. Sambo Dasuki ne ya shirya mani komai na yadda za a yi juyin mulkin. Ni shawarar juyin mulkin ne kawai na ba shi. “Na rantse da Allah. Duk shi ne ya taro mutanan da aka yi juyin mulkin da su. Duk shi ya tsara komai. Ya taka rawa a juyin mulkin sosai, a zahirin gaskiya….Sai na hada su da Sambo Dasukin, sai…kai ko a lokacin da muke shirya yanda juyin mulkin da Buharin ya zama shugaban kasa a cikin sa, zai gudana, Sambo Dasukin ne yake nemo mana kudaden da za a yi komai. “Shi ya karbo mana kudi daga wajen Aliyu Gusau, ya kuma gamsar da Kwamandan askarawan Sojin kasa, har ya aminta da shirin juyin mulkin, saboda kwabo daya ba mu samu a wajen Buhari din ba. “Ba ma wannan kadai ba, Sambo Dasukin ne ya yi amfani da kudin mahaifin shi, inda ya tura wasu Malamai kasar Saudiyya domin su je su yi addu’o’in samun nasarar juyin mulkin,” in ji Jokolo. Da yake tabbatar da abin da aka rubuta a wani littafi da aka wallafa kwanan nan mai suna, “An Encounter with the Spymaster” wanda wani mai suna, Yushau Shuaib, ya rubuta, Sambo Dasuki, ya yi bayani filla-filla kan yadda shi da kansa da kuma wasu matasan Jami’an Soji biyu, suka je suka sami Buharin a kan maganan juyin mulkin na 1983. Sambo Dasuki, ya tabbatar da cewa, “Shi da wasu matasan Jami’an Soji biyu ne (watau Manjo Mustapha Jokolo da kuma Manjo Lawal Gwadabe), suka yi takakkaka har Jos, suka iske Buharin wanda a wancan lokacin shi ne Kwamandan Rundunar Sojin tankokin yaki ta 3 da ke Jos din, inda suka yi masa bayani kan juyin mulkin na 1983 da suke shiryawa, wanda Buharin ya ci gajiyarsa inda ya zama Shugaban kasa bayan an kifar da gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari.” Sannan kuma, Sambo Dasukin ya bayyana yadda Buhari din ya nu na damuwar sa kan sakamakon kasancewar sa jagora a shirin juyin mulkin a wani taro, inda shi Sambo Dasukin ne ya tabbatar wa da Buharin da ya kwantar da hankalin sa kan duk wata barazana, inda ya ba shi tabbacin za su karbi mulkin daga hannun ‘yan siyasan.” Da Mista Shuaib, marubucin littafin, ya tambayi Dasukin, kan to ya aka yi kuma a kasa da shekaru biyu da yin juyin mulkin, sai ga shi kuma, Dasukin ya sake shiga cikin wadanda suka kitsa juyin mulkin da aka yi wa shi Janar Buharin, sai Dasukin ya bayar da amsar cewa, “Ai shi Buharin ya san ko wane ne ya kamata a zarga a kan hakan.” Dasuki ya ce, “Ni a kodayaushe nakan yi biyayya na kuma girmama na gaba da ni, da ma masu mulki duk na kan ga kimar su, lokacin ina aikin Soja da ma bayan nan. Duk da shike a lokacin, kasantuwan ni mai karamin matsayi ne, ban so a ce an je kamo shi da ni ba. Don haka ba ni cikin wadanda suka kamo shi.” “Na dai je na same shi ne a Barikin Soji na, ‘Bonny Camp,’ ni da Lawal Rafindadi. ba ta yadda zai yiwu a ce wai na ci masa mutunci kamar yadda wasu ke fadin hakan. Ina farin ciki kasancewar da yawa daga cikin wadanda suka taka rawa a lokacin duk suna raye.” Sabanin yadda ake yadawa a wurare da yawa cewa,Sambo Dasukin yana cikin Sojojin da suka je suka kamo Buharin a juyin mulkin na 1985, Kanar Abdulmumini Aminu mai ritaya, wanda dan asalin Jihar Katsina ne, ya bayyana ko su waye Manjo-Manjo din guda uku, a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin jaridar ‘Sunday Trust,’ ta watan Agusta 2015. Mai neman karin bayanin hakan, sai ya bi ta, (wannan shafin: https://goo.gl/KEz5nk, https://goo.gl/wirj2T, https://goo.gl/9bZM5A). Abdulmumini Aminu, ya ce, mutane uku ne wadanda shi da kansa ya jagorance su, suka je suka kamo Shugaban kasan na wancan lokacin, (Janar Muhammadu Buhari), sauran biyun sune, Lawan Gwadabe da kuma John Madaki. Ya ce, “Tilas na bayar da shaidar ni na jagoranci kamo shi. Na ta fi Barikin Dodon Barrack a lokacin, tare da rakiyar Sojoji biyu, Manjo John Madaki da kuma Lawan Gwadabe. Mu uku ne muka je, amma a zahiri, ni na hau sama na kamo Buharin. “Na kamo shi da cikakkiyar girmamawa, na sha karantawa a cikin kafafen yada labarai, mutane na cewa, wai mun ci mutuncin sa, mun wulakanta shi. Sam hakan ba gaskiya ne ba. Ni da Janar Buharin ne kadai muka san hakikanin abin da ya gudana a tsakaninmu a saman benen, ba wani abu makamancin hakan da ya faru. “Mun ba shi duk girmamawar da ya kamace shi a matsayin sa na babba gare mu, domin ai ko kafin wannan lokacin, muna ba shi cikakkiyar girmamawa, saboda irin halin sa. Har kawo yau, muna ganin kimarsa, babu kuma wani munafunci a tsakanin mu da shi, shi kuma ya san matsayin bin umurni a aikin Soja, a lokacin da duk na gaba da kai ya sanya ka yin wani aiki. “Ya ma taba fadi mani hakan wani lokaci. Don haka, mu kamar yadda ta faru da shi ne a baya, lokacin da ya karbi shugabanci a juyin mulkin da aka yi wa Shagari. Ina cikin wadanda suka taka mahimmiyar rawa wajen ganin ya zama Shugaban kasa, a shekarar 1983.”

Read More at: https://hausa.leadership.ng/2018/12/27/jokolo-ya-bayyana-yadda-dasuki-ya-dora-buhari-kan-mulki-a-1983-2/

Daga Leadershipayau.com

Wannan wani rahoto ne wanda jaridar Dailynigerian ta wallafa, kuma UMAR A. HUNKUYI ya fassaro mana. Rahoton yayi cikakken bayani kan yadda dasuki ya daura buhari a mulki a shekarar 1983.

Ga cikakken rahoton: Tsohon dogarin Janar Muhammadu Buhari, lokacin da ya Shugabanci kasarnan a mulkin Soja, Mustapha Jokolo, ya fasa kwai kan irin rawar da wani tsohon mai baiwa Shugaban kasa shawara Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ya taka wajen samun nasarar juyin mulkin da Sojoji suka yi a shekarar 1983, wanda shi ne ya dora Buhari, a matsayin Shugaban kasarnan na mulkin Soja a wancan lokacin.

Mustapha Jokolo, wanda tsohon Sarkin Gwandu ne wanda aka tube, ya yi wadannan bayanan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da wata jarida, a martanin da yake mayar wa kan wani littafi da Sarkin da ya gaje shi a Sarautar ta Gwandu, Janar Muhammadu Iliyasu Bashar mai ritaya, ya rubuta.

A cewar tsohon Sarkin Jokolo, Dasukin ya taka mahimmiyar rawa ta hanyar daukan nauyin juyin mulkin da kudin sa da kuma kitsa yadda juyin mulkin wanda a cikin sa ne Muhammadu Buhari ya zama Shugaban kasa, zai yi nasara a 1983. Da yake magana kan wasu bayanai da ke cikin littafin na Janar Bashar, Jokolo, ya nanata maganan na shi inda yake cewa, “A bisa zahirin gaskiya, wannan shi ya sanya nakan ji zafi sosai kan halin da Dasukin yake ciki a halin yanzun. Na damu sosai da hakan.

“Wannan gaskiyan kenan. Baccin na kawo Dasuki, cikin lamarin juyin mulkin ba, na 1983, da juyin mulkin da Buharin ya zama shugaban kasa a cikin sa bai yi nasara ba. Sambo Dasuki ne ya shirya mani komai na yadda za a yi juyin mulkin. Ni shawarar juyin mulkin ne kawai na ba shi.

“Na rantse da Allah. Duk shi ne ya taro mutanan da aka yi juyin mulkin da su. Duk shi ya tsara komai. Ya taka rawa a juyin mulkin sosai, a zahirin gaskiya….Sai na hada su da Sambo Dasukin, sai…kai ko a lokacin da muke shirya yanda juyin mulkin da Buharin ya zama shugaban kasa a cikin sa, zai gudana, Sambo Dasukin ne yake nemo mana kudaden da za a yi komai.

“Shi ya karbo mana kudi daga wajen Aliyu Gusau, ya kuma gamsar da Kwamandan askarawan Sojin kasa, har ya aminta da shirin juyin mulkin, saboda kwabo daya ba mu samu a wajen Buhari din ba. “Ba ma wannan kadai ba, Sambo Dasukin ne ya yi amfani da kudin mahaifin shi, inda ya tura wasu Malamai kasar Saudiyya domin su je su yi addu’o’in samun nasarar juyin mulkin,” in ji Jokolo.

Da yake tabbatar da abin da aka rubuta a wani littafi da aka wallafa kwanan nan mai suna, “An Encounter with the Spymaster” wanda wani mai suna, Yushau Shuaib, ya rubuta, Sambo Dasuki, ya yi bayani filla-filla kan yadda shi da kansa da kuma wasu matasan Jami’an Soji biyu, suka je suka sami Buharin a kan maganan juyin mulkin na 1983.

Sambo Dasuki, ya tabbatar da cewa, “Shi da wasu matasan Jami’an Soji biyu ne (watau Manjo Mustapha Jokolo da kuma Manjo Lawal Gwadabe), suka yi takakkaka har Jos, suka iske Buharin wanda a wancan lokacin shi ne Kwamandan Rundunar Sojin tankokin yaki ta 3 da ke Jos din, inda suka yi masa bayani kan juyin mulkin na 1983 da suke shiryawa, wanda Buharin ya ci gajiyarsa inda ya zama Shugaban kasa bayan an kifar da gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari.

” Sannan kuma, Sambo Dasukin ya bayyana yadda Buhari din ya nu na damuwar sa kan sakamakon kasancewar sa jagora a shirin juyin mulkin a wani taro, inda shi Sambo Dasukin ne ya tabbatar wa da Buharin da ya kwantar da hankalin sa kan duk wata barazana, inda ya ba shi tabbacin za su karbi mulkin daga hannun ‘yan siyasan.”

Da Mista Shuaib, marubucin littafin, ya tambayi Dasukin, kan to ya aka yi kuma a kasa da shekaru biyu da yin juyin mulkin, sai ga shi kuma, Dasukin ya sake shiga cikin wadanda suka kitsa juyin mulkin da aka yi wa shi Janar Buharin, sai Dasukin ya bayar da amsar cewa, “Ai shi Buharin ya san ko wane ne ya kamata a zarga a kan hakan.” Dasuki ya ce, “Ni a kodayaushe nakan yi biyayya na kuma girmama na gaba da ni, da ma masu mulki duk na kan ga kimar su, lokacin ina aikin Soja da ma bayan nan.

Duk da shike a lokacin, kasantuwan ni mai karamin matsayi ne, ban so a ce an je kamo shi da ni ba. Don haka ba ni cikin wadanda suka kamo shi.” “Na dai je na same shi ne a Barikin Soji na, ‘Bonny Camp,’ ni da Lawal Rafindadi. ba ta yadda zai yiwu a ce wai na ci masa mutunci kamar yadda wasu ke fadin hakan. Ina farin ciki kasancewar da yawa daga cikin wadanda suka taka rawa a lokacin duk suna raye.” 


Sabanin yadda ake yadawa a wurare da yawa cewa,Sambo Dasukin yana cikin Sojojin da suka je suka kamo Buharin a juyin mulkin na 1985, Kanar Abdulmumini Aminu mai ritaya, wanda dan asalin Jihar Katsina ne, ya bayyana ko su waye Manjo-Manjo din guda uku, a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin jaridar ‘Sunday Trust,’ ta watan Agusta 2015. 


Mai neman karin bayanin hakan, sai ya bi ta, (wannan shafin: https://goo.gl/KEz5nk, https://goo.gl/wirj2T, https://goo.gl/9bZM5A). Abdulmumini Aminu, ya ce, mutane uku ne wadanda shi da kansa ya jagorance su, suka je suka kamo Shugaban kasan na wancan lokacin, (Janar Muhammadu Buhari), sauran biyun sune, Lawan Gwadabe da kuma John Madaki. Ya ce, “Tilas na bayar da shaidar ni na jagoranci kamo shi. Na ta fi Barikin Dodon Barrack a lokacin, tare da rakiyar Sojoji biyu, Manjo John Madaki da kuma Lawan Gwadabe. 


Mu uku ne muka je, amma a zahiri, ni na hau sama na kamo Buharin. “Na kamo shi da cikakkiyar girmamawa, na sha karantawa a cikin kafafen yada labarai, mutane na cewa, wai mun ci mutuncin sa, mun wulakanta shi. Sam hakan ba gaskiya ne ba. Ni da Janar Buharin ne kadai muka san hakikanin abin da ya gudana a tsakaninmu a saman benen, ba wani abu makamancin hakan da ya faru. “Mun ba shi duk girmamawar da ya kamace shi a matsayin sa na babba gare mu, domin ai ko kafin wannan lokacin, muna ba shi cikakkiyar girmamawa, saboda irin halin sa.

Har kawo yau, muna ganin kimarsa, babu kuma wani munafunci a tsakanin mu da shi, shi kuma ya san matsayin bin umurni a aikin Soja, a lokacin da duk na gaba da kai ya sanya ka yin wani aiki. “Ya ma taba fadi mani hakan wani lokaci. Don haka, mu kamar yadda ta faru da shi ne a baya, lokacin da ya karbi shugabanci a juyin mulkin da aka yi wa Shagari. Ina cikin wadanda suka taka mahimmiyar rawa wajen ganin ya zama Shugaban kasa, a shekarar 1983.”


DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN