An Kori 'Yansanda 3 Daga Aiki Bayan Sun Yi Fashin Kudi Daga 'Dan Kasar Togo

Wasu jami'an 'yansanda guda uku da ke aiki a ofishin 'yansanda na Ijanikan a birnin Lagos sun gamu da hukunci mai tsanani na kora daga aikin 'dansanda, sakamakon aikata fashi na kudi CFA 350.000 watau Naira 221,508 kenan a kudin Najeriya.'yansandan sun kwace kudin ne a hannun wani mutum 'dan kasar Togo.

Wa'danda aka kora daga aikin 'dansandan su ne Sgt. Gbemunu Afolabi, Sgt. Afolabi Oluwaseun da Cpl. Adigun Omotayo. An kore su ne daga aiki bayan an tabbatar da laifinsu a Kotun 'yansanda na cikin gida da ake kira Orderly Rooom.

Kampanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ce, an kama wa'dannan 'yansanda ne ranar Laraba bayan sun yi ma Theodore Ifunnaya 'dan kasar Togo fashi na kudinsa CFA350.000.

Bayanai sun ce 'yansandan sun yi barazanar za su kama shi kuma su laka masa cewa ya yi fashi da makami idan ya fadi abin da suka yi masa. Wata majiya ta ace tun farko 'yansandan sun kama shi ne bayan sun sami labari cewa ya zo Najeriya ne domin ya shakata a bikin Kirsimeti.

Majiyar ta ce, bayan sun sami wa'dannan kudade a wajenshi, sai suka kwaace, suka je suka canja  kudin suka bashi N20.000 suka ce ya koma gida.

Kakakin hukumaar 'yansanda na jihar Lagos CSP Chike Oti ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma tabbatar da koran wa'dannan 'yansanda daga aiki ranar Lahadi, ya kara da cewa shi kuma mai mukamin Safeto a cikin 'yansandan, an mika lamarinsa zuwa ofishin AIG shiya ta 2 inda aka bayar da shawarar a kore shi daga aikin 'dansanda kamar yadda ta faru da 'sauran kananan 'yansanda da suka aikata laifin tare.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN