Legit Hausa
Jaridar The Nation tayi na ta
binciken na musamman inda ta fitar da hasashen zaben. Ga yadda rahoto ya
kasance a kowane yanki na kasar.
1. Arewa maso Gabas Ana tunanin cewa
Buhari zai samu kuri’u da-dama jihar Bauchi inda ya saba lashe zabe tun
fil-azal. Irin su Yakubu Dogara da sauran ‘yan PDP za su taimakawa Atiku wajen
ganin ya samu dinbin kuri’a a jihar. Haka kuma da wuya PDP ta iya doke APC a
Borno da Yobe. Sai dai Atiku na iya bada mamaki a Gombe, Taraba da kuma jihar
sa ta Adamawa.
2. Arewa ta tsakiya Masana su na
ganin cewa APC za ta doke PDP ta Atiku a jihar Neja. Jam’iyyar PDP ita kuma
tana iya lallasa Buhari a jihohin Benuwai da Kwara inda shugaban majalisar
dattawa ya fito. A jihar Filato da Kogi kuwa ba a iya cewa komai sai an tashi.
Bisa dukkan alamu kuma dai Atiku ba zai iya kawo jihar Nasarawa ba. APC tana
iya yin nasara a Abuja.
3. Arewa ta yamma Jihar Kano na
cikin inda PDP za ta samu matsala a 2019, sai dai tsohon gwamna Rabiu
Kwankwaso. Duk da APC tana cikin rikici a jihar Zamfara, zai yi wahala Atiku ya
iya yin nasara a 2019. A da can Buhari ya kan sha kash
4. Kudu maso yamma Masu hasashen
siyasa sun ce da kamar APC ce za ta lashe zaben 2019 a Legas mai dinbin kuri’u.
A jihar Ogun inda ake rikici da mutanen Ibikunle Amosun, PDP ba za ta kai
labari a zaben shugaban kasa ba, haka kuma jihar Oyo da Ondo da kuma Osun inda
Bola Tinubu yake da karfi. Ana tunanin cewa har jihar Ekiti za ta ba Atiku
mamaki a zaben na 2019.
5. Kudu maso gabas Jam’iyyar APGA ce
ta ke rike da jihar Anambra amma da wuya PDP ba ta ba Buhari kashi a jihar da
Peter Obi ya fito ba. Haka kuma APC za ta iya shan mugun kashi a jihohin Enugu
da Abia. A irin su jihar Imo, ba a iya cewa ga wanda zai yi nasara sai bayan
zaben duk da halin da APC ta shiga. Atiku Abubakar ne zai yi nasara a jihar
Ebonyi duk ta kare.
6. Kudu maso kudu A jihar tsohon
shugaban kasa Jonathan, Bayelsa, zai yi wa Buhari ya iya yin nasara a zaben
bana. A Ribas kuma babu mamaki Atiku yayi nasara, amma ba irin wanda PDP ta
samu a 2015 ba. Atiku ya fi Buhari alamun sa’a a Delta da Kuros Riba domin tun
1999, PDP ta rike da jihohin. A jihar Edo kuma da wuya, Buhari bai doke a Atiku
ba. Akwa Ibom kuma sai an tashi.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi