Rashin Ba Hazikai Dama Na Jawo Ma Jihar Kebbi Koma Baya - Bincike

Sakamakon wani bincike da isyaku.com ya gudanar a jihar Kebbi ya nuna cewa, akwai dimbin jama'a masu hazaka da ke da niyyar taimaka wa Gwamna Atiku Bagudu da kuma jihar Kebbi gaba daya, amma basu sami damar yin haka ba sabodda ba a basu fuska ba. Duk da yake an sha jin Gwamna Atiku Bagudu yana cewa " Duk wanda ke tareda ni kuma baya gaya mini gaskiya kan talakawan jihar Kebbi ba masoyi na bane".

Binciken mu har ila yau, ya nuna cewa akwai wasu mutane kalilan wa'danda ake zargin komin hazakarka sai ka biyo ta kafafunsu kafin ka iya isar da duk wani abin hazaka da kake bukatar gabatarwa ga Gwamnatin jihar Kebbi.

Har ila yau, isyaku.com ya fahimci cewa wani lokaci akan sami jinkiri wajen samun isa ga wadannan mutane, wa'danda ganin su yakan zama da 'dan nauyi, wani lokaci ma ba' asamun biyan bukata bisa manufa ta hanyar wa'dannan mutane.

Daya daga cikin misali a nan shi ne yadda har yanzu 'yan social media da ke a cikin jihar Kebbi suka kasa samar da ingantaccen manufa domin taimakawa wajen gabatar da salon yakin neman zabe na shugaba Buhari da Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi. Domin salon gabatar da rubutunsu salo ne da suke amfani da shi a yau da kullum ta hanyar cika wayoyin ma'aubuta amfani da whatsapp da hotuna da banbadancin siyasa kan Gwamna marmakin ingantaccen manuniya ga jama'a kan Gwamna Atiku Bagudu.

Hakazalika, akwai dimbin hazikan matasa da yanayi ya sa aka mance da hazakarsu, wanda wasu suna bukatar kulawa ne kalilan sakamakon haka kuma ya haifar da amfani mai yawa. Amma akasarin dalilin da ya haifar da haka shi ne rashin lissafin dauko gwanaye kan lamarin wa'danda ke da karatun abin da kuma kasancewa masana abin.

Bisa wannan dalili ne isyaku.com ya fito da wani tsari na tattara bayanai daga duk wanda zai iya bayar da gudunmuwa ga Gwamnatin jihar Kebbi da kuma Najeriya, ya zo ya yi bayani ko ya aiko mana da bayaninsa domin tantancewa.

Za ka iya tuntubarmu ta hanyar cika FORM da ke kasan wannan shafi ko ka rubuto mana bayaninka a adireshin Email isyakulabari@gmail.com

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN