Wani Babban Malamin Izala Ya Ce Shi Atiku Zai Zaba a 2019


Legit Hausa

Babban malamin addinin musulunci kuma jigo a kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Waikamatus Sunnah, (JIBWIS) Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce dan takarar shugabancin kasa na PDP Atiku Abubakar zai jefawa kuri'a a zaben 2019.

A kwana kwanan nan ne shugabanin kungiyar Izala na kasa suka bukaci 'ya'yan jam'iyyar su zabi dan takarar jam'iyyar APC, Shugaba Muhammadu Buhari a yunkurinsa na neman zarcewa karo na biyu. A hirar da ya yi da wakilin BBC, Mustapha Kaita, Sheikh fadi dalilin da yasa zai zabi Atiku Abubakar. "Zan zabi dan takarar da yafi taimakon addinin Musulunci da taimakon al'ummar kasa da amfanar da sum," a cewar Sheikh Sambo.

Babban malamin ya yi ikirarin cewa ya kwashe shekara 30 da sanin Atiku kuma ya ce Atikun ya gina masallatan Juma'a fiye da 100. Wannan ra'ayin nasa ya sha banban da na shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da ya ce kungiyar ta cimma matsayar zaben Buhari ne bayan wani taro da suka gudanar.

Shugaban masu da'awah na kungiyar, Ibrahim Jalo-Jalingo ya ce kungiyar ta cimma matsayan goyon bayan Buhari ne saboda nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fanin yaki da rashawa, yaki da 'yan ta'addan Boko Haram, farfado da noma da tattalin arzikin Najeriya.

"Al'umma sunyi na'am da nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu cikin shekaru uku da rabi hakan yasa muka yanke shawarar fadawa mambobin mu su zabi Shugaba Muhammadu Buhari da sauran 'yan takarar da ke aiki tare da shi," inji shi. A cewar babban malamin, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana kan alkibla shi yasa kungiyar Izala ke goyon bayan ta.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN