'Yansanda Sun Kama Wadanda Ake Zargin Sun Kashe Alex Badeh | isyaku.com

Rundunar 'yansandan Najeriya, ta cafke wasu daga cikin wa'danda suka kashe tsohon Kwamandan askarawan Najeriya Air Chief Marshal Alex Badeh wanda aka kashe da yammacin ranar 18 ga watan Disamba 2018, yayin da yake dawowa daga gonarsa a kan hanyar Keffi zuwa Abuja.

An sami motarsa kirar Toyota Tundra wacce aka yi ma ruwan harsashi, amma shi kadai ne aka kashe daga cikin mutum uku da ke cikin motar.

Duk da yake yunkurin manema labarai domin tabbatar da wannan rahotu ta ofishin Kakakin hukumar 'yansanda na kasa Force PRO ya ci tura, amma wata majiya mai kwari ta 'yansanda ta ce nan ba da dadewa ba 'yansanda za su gabatar da wa'danda aka kama. Majiyar ta ce " Akwai haske a wannan lamari domin mun kama wasu da ake zargi da hannu a wannan kisa, kuma za mu bayyana su ga 'yan Jarida nan ba da dadewa ba".

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post