Yadda 'Dansanda Ya Harbi Sojan Sama Da Bindiga Har Lahira A Bakin ATM | isyaku.com

Wani 'dansanda ya harbe wani sojan mayakan sama na Najeriya mai suna NAF17/32770 CPL VAL MU a bakin ATM na Bankin Unity da ke kan hanyar Marian a birnin Calabar a jihar Cross Rivers ranar Laraba 26 ga watan Disamba 2018.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Cross Rivers DSP Irene Ugbo ya ce " Lamarin ya faru ne bayan Sajen na 'yansanada da ke gadi a Bankin Unity ya ji wata hayaniya a bakin ATM na bankin da  karfe tare da arabi na safe, sai ya je domin ya gan ko miye ke faruwa. Amma isarsa ke da wuya kuma ya tambaya ko me ke faruwa sai jama'a suka rufe shi da duka, cikin wannan hayaniya ya ja kunamar bindigarsa, sakamakon haka harsashin bindigar ya sami jami'in sojan sama Val Sixtus kuma ya mutu nan take".

DSP Irene Ugbo ya ce jami'in sojin saman baya sanye da tufafin 'damara a lokacin da lamarin ya faru, haka zalika babu wanda ke sanye da tufan sojin sama a bakin wannan ATM.

Majiyarmu ta ce sakamakon namijin kokari da Kwamishinan 'yansandan jihar Cross River tare da Kwamandan sojin sama na jihar suka yi, an shawo kan rudani da hakan ya haifar ga 'bangarorin jami'an tsaron guda biyu da lamarin ya sa gashin jikinsu ya mike kuma suka fara zabure-zabure tare da tayar da jijiyoyin wuya, amma aka shawo kan wannan lamari.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN