Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka birnin Uyo na jihar Akwa Ibom da safiyar Juma'a domin kaddamar da yakin neman zabe na jiam'iyar APC mai taken "Matsayi na gaba" .
A tawagar shugaban kasa har da shugaban jam'iyar APC na kasa Adams Oshiomhole, Asiwaju Bola Tinubu, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, da sauran manyan 'yan jam'iyar APC.
Adams Oshiomhole da Rochas Okorocha sun kasa samun jituwa sakamakon yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani na mukamin Gwamna da na 'yan Majalisar wakilai na tarayya a jihar Imo. An lura cewa mutanen biyu sun kaurace wa juna duk da yake suna waje 'daya a taron na yau.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi