Karanta Abin Da Ya Faru Bayan 'Yansanda Sun Kai Samame A Gidan Dino Melaye

Rahotanni daga Abuja sun ce 'yansanda sun ja daga a kofar gidan Sanata Dino Melaye da ke wakiltar Mazabar Kogi ta yamma a jihar Kogi. Gidan Dino Melaye yana lamba 11 layin Shanga, a Maitama da ke Abuja.

Dino Melaye ya yi zargin cewa 'yansanda sun dakile kofar shuga gidansa da motocinsu, ya kuma ce akalla 'yansanda 30 ke jibge a kofar gidansa da misalin karfe 12:45 na ranar Juma'a.

Sanata Melaye dai yana daya daga cikin Sanatoci da suka dinga yi ma shugaba Buhari ihu a lokacin da yake jawabi bayan ya gabatar da kasafin kudi na 2019 ga Majalisa.

Hakazalika, 'yan kwanakin baya, Dino Melaye ya yi zargin cewa 'yansanda na shirin sace shi su yi masa allurar mutuwa, lamari da kakakin hukumar 'yansanda na kasa Jimoh Moshood ya karyata.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post