Tsohon Shugaban Kasa Alhaji Shehu Shagari Ya Rasu


Rahotanni daga jihar Sokoto sun tabbatar da cewa Allah ya yi wa tsohon shugaban kasan Najeriya Alhaji Shehu Shagari rasuwa da yammacin ranar Juma'a , wani jikansa Bello Shagari ya tabbatar da zancen, hakazalika Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasa Shehu Shagari.

Gwamna Amiu Tambuwal ya ruwaito a shafin sada zumunta cewa " Ina bakin cikin sanar da rasuwar tsohon shugaban kasa Alh. Shehu Shagari wanda ya rasu da yammacin yau a Asibitin tarayya da ke Abuja bayan wata gajeruwar rashin lafiya".

Tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ya mulki Najeriya daga 1979 zuwa 1984, ya rasu yana da shekara 93 a Duniya.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari