Fitacciyar jaridar nan ta Aminiya ta ruwaito cewa, mambobin jam’iyyar adawa ta PDP biyar sun
rasu sanadiyyar hadarin mota da ya faru a titin Sakkwato zuwa karamar
hukumar Isa ranar Litinin.
Kimanin mambobin jam’iyyar 14 ne suka samu munanan raunuka a hadarin yayin da wasu mutum 49 suka jikkata.
Mambobin
sun yi hadarin ne yayin da suke koma wa unguwar Bargaja da ke Karamar
hukumar Isa jihar Sakkwato bayan halartar kaddamar da kamfen din dan
takarar shugaban Najeriya na PDP da aka yi a dandalin Kangiwa square a
Sakkwato.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi