Type Here to Get Search Results !

Main event

Kotu ta dakatar da majalisar Kano binciken Ganduje kwata-kwata

Bisa ga dukkan alamu Gwamnan jihar Kano Ganduje ya ketare zira'in bincike da Majalisar dokoki na jihar Kano ke yi a kan badakalar cin hanci da ya bayyana a wasu fayafayin bidiyo da ya shafi Gwanan Ganduje.

Jaridar Premiumtimes Hausa ta ruwaito cewa Mai shari’a Ahmad Badamasi na babbar kotu dake jihar Kano ya yanke hukuncin dakatar da majalisar jihar Kano daga ci gaba da bincikar badakalar karbar cin hancin dala miliyan 5 da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya rika karba daga hannun ‘yan kwangila.

Idan ba’a manta ba Jaridar Daily Nigerian ta bankado badakalar karbar cin hanci da ya nuna gwamna Ganduje kuru-kuru yana karkacewa yana zura bandir-bandir din daloli na cin hanci daga hannun wani dan kwangila a aljihun jamfar shakwarar sa.

Majalisar jihar Kano ta gayyaci mawallafin wannan jarida, Ja’afar Ja’afar da ya bayyana a gaban ta domin yayi mata bayani game da wannan bidiyo da ya wallafa.

Sai dai kuma bayan haka aka shigar da kara kotu kan a dakatar da majalisar daga ci gaba da bincikar wannan badakala na gwamna Ganduje inda a kwanakin baya kotu ta umarci majalisar ta dakatar da haka har sai an yanke hukunci a kan haka.

A yau Alhamis, kotu ta yanke hukuncin dakatar da majalisar kwata-kwata daga ci gaba da bincikar gwamna Ganduje cewa wannan ba a hurumin majalisar ya ke ba.

A hukuncin da maishari’a Badamasi ya yanke, ya ce majalisar ba ta da ikon bincikar abin da ya shafi cin hanci da rashawa. Ya ce wannan yana hurumin hukumomin ICPC ne da EFCC.
Sannan kuma ya hana majalisar da kada ta kuskura ta sake kiran wani ya bayyana a gabanta bisa ga wannan magana.

Lauyan majalisar Kano, Mahmud Waziri, ya bayyana cewa ba shi da abin da zai fadi yanzu sai abin da majalisa ta yanke. Idan zata daukaka kara shi a shirye yake.

Shi ko shugaban kwamitin Bappa Dan’ agundi, cewa yayi majalisar za ta bi hukuncin shari’ar daki-daki shari’ar sannan ta bayyana matsayin ta nan ba da dadewa ba.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies