Jaridun Isra'ila sun yi caa kan Farfesa George P. Smith na jami'ar Missouri da ke Amurka,sakamakon yadda ya caccaki gwamnatin kasarsu game da zalunci da kuma gallaza wa Falasdinu da ta ke yi babu gaira babu dalili.
Smith,wanda ya
karbi goron gayyatar da Hadakan Kwararrun Masana Masu Kishin Falasdinu
suka aika masa,bayan ya halarci bikin karbar lambar yabo ta zaman lafiya
ta Nobel da aka shirya a Stockholm, babban birnin kasar Swizerland,da
zummar tattaunawa kan lamirin Falasdinu da ya ki ya ki cinyewa.
A
yayin wannan muhimmin taron, farfesan ya ce: "Isra'ila na ci gaba da
yin wancakali da dokokin kasa da kasa da kuma yin kunnen uwar shegu kan
batun janyewa ko dakatar da mamayar Falasdinu".
Masanin
ya ci gaba da cewa, "Ayyana Isra'ila da Falasdinu a matsayin kasashe
biyu masu cin gashin kansu ita ce hanya mafi sauki da kuma a'ala wajen
kawo warware bakin zaren wannan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa.A
lokacin ne za a samu dauwamammen zaman lafiya.
Haka zalika kasashen biya
zasu ci gaba da zama bakwabtan juna salim-alim ba tare wata matsa ta
sake kunno kai ba.Amma alamu na nuna mana cewa halayen Isra'ilayawa
sun sha bamban da dukannin wadannan manufofin.Sun ki yarda a cimma
masalaha, saboda basa bin sharuddan aka gindaya musu.
Idan har ana son a
zauna lafiya, to dole ta maida wa Falasdinu yankunta da ta mamaye da
kuma biya hakkokin Falasdinawa da taka.Ba zamu taba da yarda ababen da
Isra'ila ke ci gaba da yi a Zirin Gaza.Babu wani abu da Isra'ila ke yi a
yankin face gallaza wa Falasdinawa.Har ma da Yahudawa da suka ki goya
ma ta baya kan zaluncin da ta ke ci gaba da yi Falasdinawa ma, ba su
tsira daga kaidinta ba.Ya ci a ce Isra'ila ta dakatar da wannan
ta'asar".
A
bana,Farfesa Frances H. Arnold da takwarorinsa, George P. Smith
da Gregory P. Winter ne suka lashi lambar yabo ta Nobel a fannin ilimin
sinadirai,sakamakon muhimmiyar gundumowar da suka kawo a fannin cigaban
akidar juyin juya hali.
Isra'ila
ta matukar bakin cikin ganin Farfesa Smith ya lashe lambart yabo ta
Nobe.Tuni dai jaridun kasar Yahudu suka tayar da jijiyoyin wuya
kan wannan nasarar da shahararren masanin ya yi, ganin yadda ya dinka
sukar lamirin gwamnati da kuma manufofin kasarsu.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi