Legit Hausa
Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya
kallubalanci dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a
kan baddakallar cin hanci na kamfanin Halliburton. Tsawon shekaru, Hukumar yaki
da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC ta dade tana bincike a kan kamfanin
kasar Amurka wato Halliburtan kan zargin bayar da cin hanci na zunzurutun kudi
sama da $182 miliyan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A jawabin da ya yi wajen taron kasa da kwamitin kungiyoyi
masu goyon Buhari na kasa suka shirya, Tinubu ya ce ba zai yiwu 'yan Najeriya
su koma kangin bauta ba bayan an ceto su daga wadanda ke zaluntarsu. "Sun
ce mu dena magana kan abubuwan da suka wuce. Dole ne mu duba abinda ku kayi a
baya. Zamu duba batun Halliburton.
Mene yasa ta fice daga Najeriya? An kashe Dallan Amurka
Biliyan 16 a NEPA amma har yanzu wasu na cikin duhu... "Yayin da suka lura
za mu kwace mulki daga hannunsu, sun garzaya sun sayarwa 'yan kasuwan
kamfanoni, amma ni ganinsa na ke kawai sun raba wa junansu dukiyar 'yan
Najeriya ne," inji shi. A yayin da ya yi tsokaci a kan shugaban majalisar
dattawa, Bukola Saraki, Tinubu ya ce bayan ya yi amfani da APC ya lashe zabe a
2015, "Saraki ya yi amfani da kason da muka bashi domin karfafa PDP.
Hali nagari yana da muhimmanci a shugabanci. Ya fice daga
PDP, ya shigo APC, bayan ya lashe zabe sai ya sayar da kason da muka bashi
saboda bukatar kansa. Allah mai gaskiya ne amma Saraki bashi da gaskiya.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi