Neman yin kudi ta hanyar tsafi, an damke yaro da ya yi kokarin sare kan wata karamar yarinya

Dubun wani yaro ta dubunsa ta cika da safiyar yau a garin Jesse na jihar Delta bayan an kama shi dumu dumu yana kokarin sare kan wata 'yar karamar yarinya da adda saboda dalilai na tsafi domin ya sami dukiya da kudi.
 
Wani mai ba Gwamnan jihar Delta shawara Ossai Success Ovie ya shaida haka da safiyar yau.
 
Harkar tsafe tsafe gabanin zabuka 2019 sai karuwa yake yi musamman a kudancin Najeriya da ke fama da sare-saren kawunan maza da mata , wani sa'ili ma akan tube yan mata zindir kafin a kashe su kuma a yanke wasu sassa na jikinsu da suka hada da al'aura, nono da kai, kamar yadda ya faru a jihar Imo mako da ya gabata. Inda aka tsinci gawakin wasu yan mata guda biyu tsirara, da aka kashe su aka cire sassan jikinsu, daga bisani aka yar da gawarsu a gefen hanya a daji.
 
DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN