An yi ma Bukola Saraki ihu aka wulakanta shi yayin da ma'aikatan majalisa suka harzuka


Rai ya baci, kuma hankula sun tashi yayin da ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya suka yi bore a ranar Talata 4 ga watan Disamba a harabar majalisar, wanda ta kai ga sun hana yan majalisa shiga ofisoshinsu, sa’annan suka yi ma shugaban majalisar, Sanata Bukola Saraki ihu.Jaridar The Cable ta ruwaito Sanata Saraki ya gamu da fushin ma’aikatan majalisar ne a yayin da yake gabatar da jawabi a garesu, inda ya nemi su kwantar da hankulansu game da zanga zangar da suke yi akan rashin samun albashinsu.

Sai dai a yayin da yake jawabin nasa, sai ma’aikatan suka shiga yi masa eho suna cewa “Idan ba’a biyamu albashinmu ba, toh babu sauran zaman majalisa” haka suka cigaba da ihu har zuwa karshen jawabinsa. A jawabin nasa, Saraki ya baiwa ma’aikatan hakuri, inda yace su bashi daga yau zuwa ranar Juma’a mai zuwa zai shawo kan matsalar, domin a cewarsa amfanin majalisa ne ace ma’aikatanta suna cikin halin kyakkyawar walwala. 

Da safiyar Talata 4 ga watan Disamba ne ma’aikatan suka yi ma majalisar tsinke suna gudanar zanga zanga akan rashin samun hakkokinsu da suka hada da karin albashi, da sauran alawus alawus da suke bin hukumar majalisar bashi tun shekarar 2010. Wadannan korafe korafe ne yasa ma’aikatan suka nemi akawun majalisar Sani Omolari ya yi murabus daga mukaminsa saboda ya gaza kare hakkokinsu, da kuma zarginsa da suke yin a rike hakkokinsu.

Sai dai a nasa jawabin, Omolori ya bayyana ma ma’aikatan cewa ba daidai bane su hana yan majalisar zama don su gudanar da aikinsu kawai don suna zanga zanga, haka zalika ya musanta batun cewa wai ya rike musu kudadensu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Daga Legit Hausa
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN