RFI Hausa
Fadar mai martaba sarkin Kano dake Najeriya, ta sanar da nada shahararen mawaki Nazir Ahmad a matsayin Sarkin Mawakan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na biyu.
Cikin
wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan Fadar Kanon
Munir Sunusi, tace lura da gudummowar daya baiwa Sarkin Kano tun yana
matsayin Dan Majen Kano, da kuma zamowarsa Sarki, yasa ya fadar girmama
shi da wannan sarauta ta Sarkin mawaka.Fadar mai martaba sarkin Kano dake Najeriya, ta sanar da nada shahararen mawaki Nazir Ahmad a matsayin Sarkin Mawakan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na biyu.
Shi dai mawaki Nazir Ahmad ya shahara ta fuskar wakokin Sarakuna da fitattun attajirai a arewacin Najeriya amma da salon zamani, zalika yayi wasu wakokin da suka fita a fina-finan hausa
An tsaida 27 ga Watan Disamba a matsayin ranar da za'ayi bikin nadin sarautar a fadar Masarautar Kano.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI