Legit Hausa
Shugaba Muhammadu ya fasa kwan da jama'a suka dade suna
tattali. Da dadewa, jita-jita ya yadu cewa wasu mutane da ya hada da wani
gwamnan Arewacin Najeriya kamar yadda aka yada ya so Buhari ya mutu domin a
bashi kujeran mataimakin shugaban kasa.
A yau Lahadi, 2 ga watan Disamba 2018, Buhari ya bayyana
cewa yayinda yake jinya a Ingija, wasu sun garzaya wajen mataimakinsa, Farfesa
Yemi Osinbajo, domin neman kujeransa tunda Buhari ya mutu.
Yace: "Ko
Farfesa Osinbajo ya fuskanci wadannan jita-jita - Wasu sun sameshi domin ya
zabesu matsayin mataimakan shugaban kasa saboda suna tunanin cewa na mutu.
Wannan abu ya fusatashi sosai; kuma ya laburta mini lokacin da ya ziyarceni ina
jinya.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI