Wadansu masu satar mutane domi su yi garkuwa da su a babban titin Ogbakiri zuwa Buguma a jihar Rivers sun gamu da mumunar ajali a hannun jami'an yansanda bayan yansanda sun gano maboyarsu, suka kai masu farmaki kuma suka halaka su nan take kuma aka kubutar da wata ma'aikaciyar jinya Nurse yan bindigar da suka yi garkuwa da ita.
Yan bindigar sun sace ma'aikaciyar Asibitin ne tun ranar Laraba da ta gabata, amma sai ranar Talata aka kubutar da ita bayan jami'an yansanda na F-SARS sun yi ma yan bindigar diran mikiya kuma suka halaka su.
Wannan ya biyo bayan wani rahotun sirri ne da jami'an sashen ayyukan asirin kan yan fashi da makami da kuma sace mutane domin a yi garkuwa da su suka samar cikin lokaci, kan inda yan fashin suke bayan an yi amfani da kimiyyar zamani na sadarwa domin a gano hakikanin inda yan bindigar suka boye.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi