Jam'iyar APC a jihar Abia ta koka kan yadda ta yi zargin jam'iyar adawa mai mulki a jihar tana amfani da yan daban siyasa da dabbobi, domin wulakanta postocin kampen na shugaba Muhammadu Buhari da dan takarar kujerar Gwamna a jihar karkashin jam'iyar APC Dr. Uche Ogah a babban birnin jihar Umuahia.
The Nation ta ruwaito cewa wani jigo a jam'iyar APC a jihar Comrade Benedict Godson ya ce, jam'iyar APC ba za ta lamunta da irin wannan hali na takala ba bayan ya zargi jam'iyar PDP a jihar da daukar dawainiyar takala da ake yi ma yan APC.
A wani hoto da ya bayyana ma an ga awaki suna cin takardun postocin shugaba Buhari a birnin Umuahia na jihar Abia.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi