TAMBAYA:da gaske ne Allah baya karbar ibadar matar aure idan mijinta na fushi da ita domin rashin kyutatawa, biyayya ko ragowa?.
AMSA: Ga amsa da muka samo daga Malamai. An samo daga Hadisin Abdullahi Bn Amrin RA. ya ce Manzon Allah SAW ya ce 'matar da bata taba cewa na gode wa mijinta ba, matar da bata wadatuwa ga mijinta, wannan matar Allah baya kallonta a filin hisabi, wacce bata godiya ga mijinta inji Annabi Muhammadu SAW, matar da bata godiya ga mijinta, bata wadatuwa da mijinta , duk abin da ya yi mata tana kushe masa Hadisin ya inganta, ka duba Silsilatul Sahiha Hadisi na 289.
A karkashin sharhin wannan Hadisi, Muhammad Nasir Bn Albany cikin Silsilatul Sahiha Mujalla na farko shafi na 518 ya kawo Hadisin Abdullahi Bn Umar RA, ya ce Manzon Allah SAW ya ce akwai mutane guda biyu Sallar su bata wuce daidai kan su, na daya shi ne Bawa da ya guji Uwayen gidansa, Sallarsa Allah baya karbarta hatta sai ya dawo wajen Uwayen gidan nasa.
Na biyu kuma ita ce matar da ta saba wa mijinta, Allah madaukaki baya karbar Sallar ta, hatta sai ta koma ga mijinta ta nemi gafararsa. Wannan Hadisi ya inganta yana cikin Sahihul jami'ul Sagir Hadisi na 136 da kuma Silsilatul Sahiha Hadisi na 288.
Annabi SAW ya ce matar da bata godiya ga mijinta, wannan mata Allah baya kallonta a filin hisabi, sannan Hadisin Abdullahi Bn Umar ya ce Allah baya karbar ibadar wannan mata, duk Sallar da take yi, wallahi Allah SWA baya karba hatta sai ta koma ga mijinta ta bashi hakuri.
Latsa Nan Ka Saurari Sauti (Bayan ka latsa sai ka kara muryar wayarka, kuma ka dan jira manhajar sauti zai fara aiki)
Daga Nasihar Haifan Jos
Hadawa da wallafawa Isyaku Garba
Daukan nauyin gabatarwa: Alhaji Umar Namashaya Diggi, shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo a jihar Kebbi ne ya dauki nauyin shirin. Allah ya saka masa da mafificin alkhairinsa Amin.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi