Rigimar manya sai manya, musamman ga harkar siyasar Najeriya, domin dai a yanzu da aka fara yakin neman zabe na shugaban kasa a fadin Najeriya, kalamai ne kake ji kamar tatsuniya, domin wannan karo, dan takarar kujeran shugaban kasa a jam'iyar PDP Atiku Abubakar ne ya caccaki shugaba Buhari.


Jaridar Premium Times Hausa ta ruwaito cewa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina yarda da tatsuniyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi musu, domin ya kasa cika alkawurran da shi da jam’iyyar sa suka dauka a 2015.

Atiku ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke jawabi ga dandazon magoya bayan jam’iyyar PDP a wurin kaddamar da kamfen na yankin Kudu maso Yamma, a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

A wurin taron akwai shugaban PDP na kasa, Uche Secondus, dan takarar mataimakin shugaban kasa, Peter Obi, tsoffin gwamnonin Ekiti da Cross Rivers, Ayo Fayose da Liyel Imoke, da kuma ‘yan takarar gwamna a karkashin PDP, na jihohin Lagos da Oyo, Jimi Agbaje da Seyi Kehinde.
Akwai irin su Gbenga Daniel da sauran manyan PDP na Kudu maso Yamma.

Atiku ya ci gaba da cewa za su tabbatar Buhari bai dawo yin zango na biyu ba, sai dai ya zarce Daura bayan zaben 2019.

Ya ce Buhari ya kasa cika alkawurran da ya dauka da wanda jam’iyyar APC ita kanta ta daukar wa ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zaben 2015.

“Bari na shaida muku cewa nan da watanni biyu za ku je ku zabi shugabanni. Don haka ku yi aiki da hankulan ku, kada ku zabi APC, saboda ta kasa cika alkawari. An ci moriyar dimokradiyya a lokacin PDP fiye da yanzu lokacin APC.

“APC ta yi alkawarin samar da ayyuka ga matasa milyan 12, amma ba a fuskantar komai a yanzu sai rashin aiki da kuma matsananciyar yunwa.” Inji Atiku.