Fusatattun matasa sun yi wa Buhari wakar "jiki magayi" a jihar Zamfara


Legit Hausa

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta bayar a sanarwar takaita zirga-zirga a karamara hukumar Tsafe da ke jihar sakamakon zanga-zangar nuna damuwa kan yawaitar kashe-kashe a jihar wadda daga bisani ya haifar da rudani da kone-kone.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu matasa sun fito suna zanga-zangar nuna damuwar su kan lamarin rashin tsaro a jihar inda aka ce sun rufe tittin da ya sada Funtua, Zaria, Sokoto, Kebbi da Kaduna. Rahotanni sun ce matasan sun kona sakatariyar karamar hukumar Tsafe kuma sun nufi gidan shugaban karamar hukumar.

Matasan sun rera wakar, "jiki magayi, sai mun canja Buhari", kamar yadda zaku iya gani a cikin Jami'n hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, Mohammad Shehu ya sanar da cewar an al'umma za su iya fitowa suyi harkokinsu ne daga karfe 7 na safe zuwa karfe 6 na yamma kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Ya ce dokar takaita zirga-zirgar za ta cigaba da aiki har sai nan gaba idan abubuwan sun lafa a garin. 'Yan ta'adda sun kai hari a kauyen Magami da ke karamar hukumar Maradun a ranar Asabar inda suka kashe mutane da dama.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN