Kebbi: 'Yansanda sun kama daya daga cikin 'yan fashi da suka yi sata a Sandare suka gudu

Rundunar 'yansandan jihar Kebbi, ta yi nassarar cafke daya daga cikin 'dan gungun 'yan fashi da makami da suka shiga gidan Alh. Shehu Sandare suka yi fashin Naira miliyan biyu da dubu dari biyar a kauyen Sandare da ke karkashin karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi da dare ranar Talata 19 ga watan Disamba 2018.

An bizine gawakin yan fashi 2 da aka kashe a Sandare na karamar hukumar Kalgo jihar Kebbi 

Idan baku manta ba, mun kawo maku labari kan yadda gungun 'yan fashin kimanin mutum 10 suka shiga kauyen Sandare cikin dare suka yi fashin kudi, amma wasu mutum biyu daga cikin 'yan fashin suka ci karo da mumunar ajali, domin daga karshe jama'ar gari sun kashe biyu daga cikin 'yan fashin.

Saidai 'yansanda sun kama daya daga cikin sauran 'yan fashin da suka tsere, kuma yana fuskantar bincike a hedikwatar 'yansanda da ke Gwadangaji, a Jihar Kebbi.DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Previous Post Next Post