Sojin Ruwan Najeriya Sun Cafke Wasu Barayin Da Ke Hakar Danyen Man Fetur | isyaku.com

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta cafke wani jirgin ruwa dauke da haramtaccen man fetur da aka haka ba bisa ka'ida ba, kuma ta mika jirgin da wa'danda aka kama ga jami'an hukumar EFCC shiyar Benin domin gudanar da bincike.

Wa'danda aka kama sun hada da Promise Onate, Emonefe Stanley, Samson Obaje da kuma Peresey Friday. An kama mutanen ne a jirgin ruwa MV Enterprise, makare da 'danyen man fetur, bayan jami'an sojin ruwa da ke sintiri a jirgin ruwa NNS Delta, dauke da mayakan ruwaan Najeriya sun bincike jirgin MV Enterprise, sai suka gano cewa mutanen sun yi satar hakar 'danyen man fetur ne.

Kwamandan jirin ruwan sojin Najeriya Captain P. G. Yilme ne ya shaida wa manema labarai haka, yayin da yake mika mutanen da jami'an sa suka cafke ga jami'an EFCC a Warri na jihar Deltaranar 24 ga watan Disamba 2018.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post