Ledit Hausa
Kasar Amurka ta bawa tsohon dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar izinin shiga kasar wato biza. A cewar The Cable wani daga cikin iyalin tsohon shugaban kasan ya tabbatar da cewa an bashi takardan izinin shiga kasar.
Kasar Amurka ta bawa tsohon dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar izinin shiga kasar wato biza. A cewar The Cable wani daga cikin iyalin tsohon shugaban kasan ya tabbatar da cewa an bashi takardan izinin shiga kasar.
A watan Oktoba, Direkta Janar na yakin neman zaben Atiku
Presidential Campaign Organisation (APCO), Gbenga Daniel ya yi ikirarin cewa
Amurka ta fadawa Atiku cewa zai iya neman bizar. A yayin da ake yi tambaya a
kan batun a ranar Juma'a, Jami'in hulda da jama'a na ofishin jakadancin Amurka
da ke Legas, Brussel Brooks ba yi tsokaci kan batun ba inda ya ce sirri ne.
A baya, an ganin kamar Atiku ba zai iya shiga Amurka ba
saboda ana zargin cewa ya hada baki da wani dan majalisa a Amurka, William Jefferson
wajen karbar rashawa kuma shi dan majalisar an tabbatar da laifinsa a Amurka.
Duk da cewa Atiku ya jadada cewa bai aikata wani laifi ba, jam'iyyar All
Progressives Congress (APC) ta dade tana kallubalantarsa ya tafi Amurka idan
har ya tabbatar bashi da laifin.
A ranar Alhamis, Ministan yada labarai na Najeriya, Lai
Mohammed ya gargadi Amurka da kada da sake ta bawa Atiku visa idan har ba ta
son nuna fifiko tsakanin 'yan takarar shugabancin kasa na shekarar 2019. An
ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta taka muhimmiyar rawa
wajen ganin Amurka ta bawa Atiku izinin shiga kasar.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI