Shekara 20 tana dauke da cutar HIV, karanta abin da ta ce game da cutar | ISYAKU.COM

Jaruma kuma mai gabatar da shirye shirye a wani gidan Talabijin a kasar Afrika ta kudu Criselda Kananda-Dudumashe, ta ce tana dauke da kwayar cutar HIV fiye da shekara 20, kuma haka bai sa ta karaya ba.

Ranar daya ga watan Disamba zai kasance ranar masu dauke da cutar HIV a Duniya.

Criselda ta ce "yanzu haka ina dauke da wannan cuta tsawon shakara 20 kenan, kuma ina gudanar da rayuwata kamar kowa, cikin kwanciyar hankali da kulawa.

Shi ya sa nike fadakar tare da ilmantar da jama'a gaskiyar lamarin wannan cuta, amma wasu sukan yi mani bahaguwar fahimta har ma sukan yarba mani kalamai masu zafi, amma ya zama wajibi in jure duk wannan tsangwama, kuma in fahimtar da su manufata kan ababen da ya kamata su sani dangane da wannan cuta domin ta haka kawai zan iya sa su fahimce ni kuma su gane".

Criselda ta ce kada jama'a su shiga damuwa balle su takura kansu domi sun kamu da cutar HIV. "Ba dole sai ta jima'i ne ake iya kamuwa da wannan HIV ba, kuma domin ka kamu da cutar ba shikenan ne karshen rayuwa ba domin ga ni nan daram kuma ina dauke da wannan cuta har tsawon shekara 20".

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN