Wata babban Kotun tarayya a garin Birnin kebbi ranar Alhamis, ta bayar da umurni hukumar EFCC ta tasa keyar tsohon Gwamnan jihar Kebbi Alh. Sa'idu Nasamu Dakingari tare da wasu mutum biyu zuwa wajen ajiye wadanda ake tuhuma na hukumar a garin Birnin kebbi har zuwa ranar 10 ga watan Disamba kasancewa ranar zaman Kotun na gaba kan shari'ar.
Wanan yana da alaka ne da shari'ar da ake yi ma Sa'idu Dakingari, Sunday Dogonyaro da Garba Kamba kan tuhume-tuhume 13 da EFCC ke yi masu kan zargin badakalar Naira Miliyan 450 da suka karba daga tsohuwar Ministan albarkatun mai na Najeriya Deizani Alison Madueke.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi