Wasu soji da dama sun yi shahadar soji sakamakon harin yan ISWA a Maitile

Rahotu da muka samu daga Arewa maso gabas ya nuna cewa ana fargaban cewa fiye da soji goma ne suka biya babban farashin yi wa kasarsu hidima bayan sun mutu sakamakon hari da kungiyar ISWA ta kai wa Bataliya ta 157 da ke Maitile a jihar Borno ranar Asabar,.

Ana fargaban cewa maharan sun yi awon gaba da wasu makamai kamar yadda wata majiya ta shaida wa TheCable. Majiyar ta ce galibin sojoji da suka mutu a wannan hari wadanda suka tsaya ne domin su fuskanci wadannan maharan.

Hakazalika majiyar ta ce ana fargaban an kashe kwamandan wannan Bataliya, amma ba tabbacin haka kamar yadda wata majiya ta kara shaida wa TheCable.

Rahotanni sun ce Gen.Texas Chukwu, Kakakin hukumar soji, bai amsa kiran wayar salula da akayi masa dangane da lamarin ba, haka zalika bai mayar da amsar sakon SMS da aka aika masa ba.

Dakarun soji sun fuskanci irin wannan hari makonni kadan a Kukawa.

Ammma sanannen lamari ne cewa sojin Najeriya sun dakile kaifin hare-hare na kungiyoyi masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso gabas a Najeriya, sakamakon kulawa da gwamnatin shugaba Buhari ta ba mayakan sojin Najeriya da ke fuskantar hare hare daga kuniyoyin ISWA da Boko Haram a wannan yanki.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN