Salisu Garba Koko ya fice daga APC zuwa SDP, tsayawarsa a APC ya fi - jigon APC a Kebbi

isyaku.com 21-11-2018

Dan majakisar tarayya mai wakiltar Maiyama da Koko Besse Alh. Salisu Garba Koko, ya canja sheka daga jam'iyar APC zuwa jam'iyar Social Democratic Party of Nigeria SDP. Alh Salisu ya shaida mana a tattaunawa ta wayar tarho cewa shi da dimbin magoya bayanshi sun canja sheka zuwa jam'iyar SDP. Dan Majalisar ya koma jam'iyar adawa ta SDP ne tare da dimbin magoya bayansa.

Majiyarmu ta gano cewa, ficewar Alh Salisu daga jam'iyar APC yana da nassaba da yadda lamurra suka kasance a lokacin zaben fitar da gwani da jam'iyar APC ta gudanar a jihar Kebbi wanda da dama daga cikin yan Majalisar wakilai na tarayya suka rasa tikitin sake komawa kan Kujerinsu, domin dai sakamakon wannan zaben ya nuna cewa wadannan yan Majalisa sun sha kasa.

Saidai shugaban jam'iayar APC na jihar Kebbi Arch. Bala Sani Kangiwa, ya shaida mana cewa " na gani a Social Media cewa Salisu Garba Koko ya canja sheka zuwa jam'iyar SDP, amma da yake bayanin a Social Media ne, ba a faye gaskata lamarin ba, kuma bai rubuto mana ba cewa ya fice daga jam'iyar APC".

"Bamu fatar mu rasa daya daga cikin yayan mu, amma kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da dama mutum ya shiga jam'iyar da yake so, sakamakon haka bamu da ikon mu hana shi barin jam'iyar APC, balle irinshi wanda ta jam'iyar APC Allah ya bashi dama ya je Majalisar tarayya. Sakamakon haka idan abu ya faru, kamata ya yi a yi hakuri. Duk abin da Allah ya dora wa bawa ba makawa sai ya faru.Lokacin da ya tafi Majalisa, akwai da yawan mutane da suka so wannan mukamin, amma shi ne Allah ya zaba kuma aka yi hakuri".

Arch Bala Sani ya ci gaba da cewa " Sakamakon haka ba dadi a ce dan jam'iya idan ya rasa mukami sai ya fita daga jam'iya, ai wannan ba daidai bane. Amma mu bamu ji dadi ba ya bar jam'iya ya koma wata jam'iyar, amma dai har yanzu ba'a makara ba, muna fatar ya dai yi hakuri ya zauna a cikin jam'iyar APC ya fi, domin mu dai bamu son mu rasa kowaye, ko mutum daya ne, domin kowa yana da muhimmanci ga harkar siyasa".

Daga Zuwaira Abubakar da Isyaku Garba


DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN