Yan bindiga sun kashe wani matuki motar Hilux suka sace dansa a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara na nuna cewa an kashe direban wata motar Hilux kuma aka sace dansa. An kashe Alh.Muhammadu Danbuzu Kaura da sanyin safiyar Litinin yayin da yake dawowa Kaura Namoda daga Sokoto.

Daga bisani yan bindigan su yi awon gaba da dansa Abubakar Danbuzu, amma bayanai sun ce an gano motar a hanyar Shinkafi da safiyar Talata.

Yanuwan Abubakar sun sami kiran waya daga wadanda suka sace shi, amma babu wani karin bayani kawo yanzu.
 
DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

0/Post a Comment/Comments

Rubuta ra ayin ka

Previous Post Next Post