Legit Hausa
A farkon watan nan, Wasika daga hukumar albashi ya nuna cewa
an karawa jami’an yan sandan Najeriya albashi. Shugaba hukumar Cif Richard
Onwuka Egbule, ya rattaba hannu kan wannan wasika bayan samun umurni daga
ofishin hukumar. Wasikar tace:
“Ina mai tabbatar da Karin albashi da canjin tsarin albashin
hukumar yan sanda. Wannan kari zai fara aiki ne daga ranan 1 ga watan Nuwamba,
2018 kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar.” Yayinda karban bakuncin
shugabannin hukumar yan sanda inda suka zo godiya a yau, shugaba Buhari ya
bayyana cewa:
“Daga Taraba zuwa Sokoto, zuwa Kudu maso kudu, mutane na
cikin tsoro idan basu ga sojoji ba. Ina farin cikin Karin albashi da alawus da
sa ran cewa hakan zai kara hazaka da kokarin yan sanda da kuma karfafa tsaron
cikin gida.” “A bar sojoji su dinga manyan ayyuka, ya kamata yan sanda su iya
dakile laifuka irinsu fashi da makami, garkuwa da mutane, da sauran su. A
kowani kauye, akwai yan sanda a wajen.”
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI