Kungiyar Iyaye mata masu ciyar da daliban jihar Kebbi sun yi tattakin neman gwamnatin ta biya su

isyaku.com

Kungiyar Iyaye Mata Yan Fidin (feeding) KIMYF 2015 na jihar Kebbi, sun gudanar da wani tattaki a garin Birnin kebbi ,daga bisani suka yada zango a gaban gidan Gwamnatin jihar Kebbi. Yan kungiyar suna kira ga Gwamnatin jihar Kebbi ne cewa ta biya su kudaden kwangilar ciyar da dalibai yan makarantar sakandare da suka yi daga watan Nowamba 2014 da kuma watan Janairu zuwa watan Mayu 2015, watau shakara uku da suka gabata.

Shugaban tattakin na yau kuma shugan kungiyar KIMYF a jihar Kebbi yankin Bunza, Hajiya Maryam Umar, ta shaida mana cewa " Muna rokon Gwamnatin jihar Kebbi ta yi wa Allah ta biya mu kudaden kwangilar ciyar da dalibai da muka yi, musammam mu mata 'yan kwangilar ciyar da dalibai yan makaranta. Yanzu haka wasu daga cikin mu sun gamu da lalurar shanyewar bangaren jiki watau Paralysis. Wasu kuma sun kasa aurar da yayansu mata sakamakon rashin kudi domin mun riga mun yi kwangilar ciyar da dalibai daga bisani kuma ba'a biya mu kudadenmu ba.

Hakazalika wasu daga cikin yayan mu suna zuwa makarantar kudi, amma sakamakon wannan lamari na rashin biyanmu kudadenmu yanzu wasu yaran basa ko iya zuwa makarantar Gwamnati.Muna kira ga Maigirma Gwamna ya taimaka ya biya mu kudadenmu, idan ma ba'a sami biyanmu ribar kwangilarmu ba, don Allah a biya mu uwar kudaden da muka kashe domin mu ci gaba da gudanar da rayuwa cikin daraja kamar kowa".

Mujallar isyaku.com ya lura cewa, yara kanana ne suka fi yawa a wannan tattaki, amma Hajiya Maryam ta ce, " Saboda rashin sukunin zuwa daga iyayensu sakamakon wasu matsaloli da suka hada da  na rashin lafiya, shi ya sa iyayensu wadanda yan kwangilar ciyar da daliban ne suka turo yayansu domin su waakilcesu saboda tare ake shan wahala sakamakon rashin biyan kudaden".

Daga bisani dai, majiyar mu ta ce bayan masu tattakin sun isa Gidan Gwamnati, ba'a bari suka shiga ba, wani jigo a siyasar jihar Kebbi, ya lallashi matan , ya kuma yi alkawari cewa zai shaida wa Gwamnan jihar Kebbi wannan zance. Wannan ya biyo bayan yadda matan suka fashe da koke koke  yayin da suke gabatar da jawabi a gaban gidan Gwamnati

Tattakin na yau ya kunshi yan kwangila mata zalla ne wadanda suka yi kwangilar ciyar da dalibai na makarantun sakandare a jihar Kebbi daga ajin JSS1 zuwa SS3.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN