Shugaba Muhammadu Buhari ya kalubanci ragowar shugabannin
kasashen gefen tekun Chadi (LBC) a kan kara rubanya kokarinsu a bangaren yaki
da 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram. Buhari ya yi wannan kira ne a yau, Alhamis,
yayin halartar taron shugabannin kasashen gefen tekun Chadi a birnin
N'Dajamena.
"Ba zamu saurara ko mu bar makiya yankin mu su
sukurkuta zaman lafiya a kasashen mu ba. Dole mu kara kokarinmu domin korar
ta'addanci daga yankinmu." "Dole mu tashi tsaye wajen samar da zaman
lafiya da cigaba mai dorewa.
A wannan gaba ne nake bukatar mu hada karfi da karfe domin
ganin mun kakkabe ragowar 'yan ta'adda daga yankin mu," a kalaman Buhari.
Taron ya samu halartar shugabannin kasashen Chadi, Nijar, da Kamaru. A baya
legit.ng ta sanar da ku cewar a yau, Alhamis, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari
ya tashi zuwa N'Dajamena, babban birnin kasar Chadi, domin shugabantar taron
shugabannin kasashen Afrika dake da makwabtaka da tekun Chadi (LBC).
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta rawaito cewar
Buhari ya yi amfani da matsayinsa na shugaban kungiyar kasashen wajen kiran
taron domin tattauna yadda za a samu zama zaman lafiya mai dorewa a rukunin
kasashen LBC dake fama da hare-haren 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram. A wata
sanarwa da Femi Adesina, karamin kakakin shugaba Buhari, ya fitar a Abuja ya ce
za a yi taron ne yau, Alhamis, a N'Dajamena.
Adesina ya bayyana cewar an gayyaci shugaban kasar Benin
zuwa wurin taron saboda kasar sa ta bayar da gudunmawar sojoji domin yakar
aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram. A cewar Adesina, taron na kwana daya
zai tattauna yanayin tsaro a tsakanin kasashen da niyyar samar da hanyoyin da
za a bi domin kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI