Hukumar Sojin Najeriya ta ce jami'anta sun gano wani
haramyaccen sansanin bayar da horo na fada da bindiga a Nonwa Gbam (sansanin
horas da 'yan yiwa kasa hidima) a karamar hukumar Tai da ke jihar Rivers.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar dattawan Ogoni sun zargi
Ma'aikatar Muhalli na Kasa da kawo dakarun sojoji zuwa garuruwan Ogoni domin
samar da tsaro yayin da ake aikin tsaftace garuruwan da danyen man fetur ya
gurbata.
Legit Hausa
Mataimakin Direktan yada labarai na sojin, Aminu Iliyasu ya
ce dakarun sojojin sun gano sansanin bayar da horon ne yayin da suke kewaya
garin. "Dakarun sojin sun sama matasa fiye da 100 da ake bawa horo irin na
soji," inji shi. "Hukumar Sojin tare da hadin gwiwa da sauran
hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike domin binciko wadanda ke daukan
nauyin 'yan bindigan da kula da sansanin."
Ya kara da cewa sojin ta gano haramtattun sansanin bayar da
horo masu kamanceceniya da wannan a jihohin Benue da Taraba a farkon wannan
shekarar kuma an dauki mataki a kansu saboda tattabat da tsaro. A martaninsa ga
wannan lamarin, Gwamnan jihar, Nyesome Wike ya ce Hukumar Sojin Najeriya ta
zama makami da 'yan siyasa ke amfani da ita domin kuntatawa talakawan Najeriya.
Ya ce tarwatsa sansanin bayar da horon na jihar Rivers da
Soji su kayi rashin sanin ya kamata ne kuma zai iya haifar da rashin zaman
lafiya a jihar. "Sojin ba su damu da yadda Boko Haram ke kashe sojojin mu
a Borno ba. Sun mayar da hankali ne wajen tayar da fitina a jihar Rivers.
"Idan ba ku son a zauna lafiya a Rivers, toh sauran sassan Najeriya ma ba
za a samu zaman lafiya ba.
Suna son suyi amfani da bindigogin su domin kashe mu,"
inji Wike. Wike ya ce gwamnatin jihar ta hada gwiwa da Hukumar Yan sanda, DSS
da sauran hukumomin gwamnatin tarayya wajen kafa 'yan bangar jihar Rivers 'Rivers
State Neighbourhood Safety Corps Agency.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI