• Labaran yau


  Maganin zazzabin cutar Typhoid | Mujallar isyaku.com

  Meela's Blog

  Assalamu Alaikum,yau zamu yi magana ne dangane da abinda ya shafi zazzabin Typhoid, yanda ake kamuwa da shi, da yanda za a magance sa.

  Zazzabin Typhoid wani ciwon ne mai wuyar sha'ani, da ake daukar sa ta kwayoyin Bacteria mai suna Salmonella typhi. Anfi samun wannan ciwon akasashen masu tasowa. Kungiyar Lafiya ta duniya ta kiyasta cewa mutune miliyan 22 ne a duniya ke fama da wannan zazzabin na Typhoid, haka kuma mutun 200,000 sukan rasa rayukan su akowace shekara. 
  ME KE KAWO ZAZZABIN TYPHOID?

  Bincike ya nuna ana kamuwa da wannan cutar ta hanyar wasu kwayoyin halitta da ake kira salmonella typhi wayanda ake samun su ta hanyar gurbataccen ruwa, ko abinci marar tsabtaa. Ayayin da mutum yaci wani abinci ko wani abin sha mai dauke da wannan kwayoyin cuta to sukan tafiya zuwa yan hanjin mutum daga nan kuma sai su watsu zuwa cikin jinin mutum inda zasu sami damar yaduwa zuwa hantar mutum da kuma wasu sassa na jikin dan adam daga nan kuma sai su cigaba da hayayyafa.
  Bincike ya nuna cewa ba daga shigar kwayoyin cutar suke haddasa ciwo ba, sukan dauki sati daya zuwa biyu kafin mutum ya fara ganin alamomin ciwon su bayyana a gareshi.

  ALAMOMIN ZAZZABIN TYPHOID


  CIWON KAI: Mutun zai rika fama da ciwon kai akoyaushe, wani ko ya sha magani baya sauka, wani yakan sauka na dan lokaci, kafin ya dawo.

  CIWON CIKI: Yawan ciwon ciki alama ce da ke nuna mutun ya kamu da zazzabin typoid, zaka samu kanka da murdawar ciki, wani lokaci har da ciwon mara, zaka ji hanjin ka na kuka wani lokaci har sai mutun ya ziyarci bayi da sauran su.

  RASHIN KUZARI: Mutun zai kasance akoyaushe ba shi da wani kuzari, aiki kadan zai yi sai gajiya.

  Rashin jin dadin abinci yana daya daga alamomin kamuwar cutar typhoid

  YANDA SANGA-SANGA KE MAGANCE ZAZZABIN TYPHOID

  Masana maganin gargajiya sunyi gwaji akan yanda ganyen sanga sanga ke maganin zazzabin typooid. 
  Za asamu ganyen sanga sanga a wanke sa da ruwa masu tsabta, atafasa sa. Bayan an tafasa za a sauke a tace ganyen in ya huce a maida su ruwan sha.
  Akan daka ganyen sa a tace ruwan ba tare da an tafasa ba.
  Akan yi kunu da shi ana sha, ana kuma iya dafawa arika suraci da wanka da shi. 
  Bayan  maganin ciwon typhoid da sanga sanga ke yi, bincike ya nuna cewa sanga sanga yana kashe kwayoyin plsmodium musamman falcifarum dake kawo zazzabin malaria na cizon sauro wato dai baya ga kasancewa sanga sanga na maganin typhoid to kuma yana maganin malaria.
  RIKAKAFE


  Mu kula da tsabtace muhallin mu, musanman ruwan shan mu, da kuma abincin mu. Mukan iya tafasa ruwan mu na sha kafin muyi amfani da su, wannan hanya ce sosai da za ta taimaka wurin rage yaduwar wannan ciwo. haka kuma rage cin abincin sayarwa Wanda ba a tabbatar da tsabtar sa ba.
  Allah ya bamu lafiya yasa mu dace.  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Maganin zazzabin cutar Typhoid | Mujallar isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama