Hausawa sun ce soyayya ruwan zuma ce, wata mata farar fata, Heidi Hepworth yar shekara 45 yar kasar Britaniya ta Musulunta sakamakon tsunduma cikin soyayya da ta yi tare da Mamadou Salieu Jallow wani matashi dan shekara 31 daga kasar Gambia, kuma Musulmi.
Wannan matar ta hadu da saurayinta ne a shafin Facebook, daga bisani kuma soyayya ta yi karfi har ya kai ga cika sharuddan aure tsakaninsu.
Sakamakon haka Heidi Hepworth ta bar kasar Britaniya a cikin jirgin sama zuwa kasar Gambia har saau hudu domin shirye shiryen aure da wannan dan kasar Gambia kuma bakar fata.
Bayanai sun ce ta haifi yara 6 tare da tsohon mijinta, kuma sun rabu da shi bayan sun shfe shekar 23 tare.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI